Waye ya kashe sheikh jafar da sheikh Albania Zaria? Malam Datti Assalafiy


Na rantse da Allah 'yan Boko Haram ne suka kashe sheikh Ja'afar Kano, sune kuma suka kashe sheikh Albaniy Zaria
Akan kisan Malam Ja'afar wallahi su 'yan Boko Haram da kansu suka tabbatar mana da haka, cikin wadanda suka fada cewa sune suka kashe Malam Ja'afar akwai Mamman Nuur Alqadi (kunsan waye Mamman Nur ai a cikin sha'anin Boko Haram)

'Yan Boko Haram ko ince wani bangaren 'yan Boko Haram wadanda sune asalin wadanda suka kafa kungiyar tun a shekarar 2002 wadanda akafi sani da " 'yan Kanamma" sune suka kashe sheikh Ja'afar Mahmud Adam (Rahimahullah), su 'yan Boko Haram din da kansu sun tabbatar da hakan, duk da cewa suna da sabani kan cewa jinin sheikh Ja'afar ya halatta ko bai halatta ba? Amma wallahi sune suka kashe shi
Su wadannan 'yan Boko Haram wato 'yan Kanamma a wancan lokaci, sai sukaje sukayi tunga a FANSHEKARA sukayi ta kashe jami'an tsaro kafin da sukaga za'a cimmasu sai suka sulale suka koma SAHARA can yankin Algeria/Mali, domin tun lokacin da aka tarwatsasu a garin Kanamma dake jihar Yobe inda anan ne aka kashe shugabansu na farko wato Muhammad Ali.
To sauran wadanda suka tsere daga wannan fadan tsakaninsu da jami'an tsaro sai suka gudu sukabar Nigeria suka koma Algeria inda suka hadu da kungiyar Alqa'idah dake Magrib (AQMI) anan ne suka samu horo na yaki da yanda ake kera bomabomai, to su wadannan mutane sune suka dawo suka kashe Malam Ja'afar Mahmud Adam (Rahimahullah)
Kuma a wancan lokaci basa tare dasu Muhammad Yusuf, a wani lokacin kafirtashi sukeyi, amma daga baya sun hadu da mutanen Muhammad Yusuf din, kuma bayan mutuwarsa sune sukayi ta horar da 'yan Boko Haram da koya musu yadda ake hada bomabomai
Cikin wadannan mutane 'yan Kanamma da suka kashe sheikh ja'afar akwai UQUBA Ibrahim Al-Muhajir hotonsa ne mai lamba na biyu (2) da na daura cikin wannan rubutu, wanda daga karshe sojoji sun samu nasarar kashe shi a garin Bama jihar Borno, amma har yanzu markazinsa (UQUBAH) yana nan yamma da farisu kusa da inda Shekau yake boye a halin yanzu haka.


Kuma kamar yadda na fada a baya, 'yan Boko Haram da yawane suka tabbatar da wannan labari cikinsu har da Mamman Nuur Alqadi, kuma har ya tabbatar da cewa su bangaren su Muhammad Yusuf basu da hanu wajen kisan sheikh Ja'afar, kai da farkoma har sunayiwa 'yan Kanamma din inkarin cewa basu kyauta ba da suka kashe shi, kuma shiyasa har su Mamman Nur da tawagarsa sukaje ta'aziyyar rasuwan Malam Ja'afar
Amma daga baya su dinma su Mamman Nur wai sun gano cewa ashe kashe Sheikh Ja'afar da 'yan uwansu 'yan Kanamma sukayi daidai ne, domin wai kafirine malamin gomnati, don haka jininsa (sheikh ja'afar) ya halatta a zubar
Daga cikin abinda zai tabbatar da cewa 'yan Boko Haram ne suka kashe sheikh Ja'afar shine bayan sun kasheshi ai sunci gaba da kashe Malaman Ahlussunnah, misali a cikin Maiduguri kadai imba Allah ba babu wanda yasan adadin malaman da suka kashe, misali kisan Malam Ibrahim Gomari, Malam Bashir Kacalla da sauransu
Kuma kisan Sheikh Albaniy Zaria ya dada bayyanawa al'umma karara cewa sune suka kashe Malam Ja'afar, domin idan aka dubi salon da sukabi suka kashe malaman duk yana kama da junta.
Shekarar da ta gabata nayi wani rubutu sharhi akan kisan Sheikh Albaniy Zaria wanda na daura alhakkin kisan akan 'yan Boko Haram, daga cikin abinda nace shine kamar haka;
!
Shekarar da 'yan Boko Haram suka shiga cikin Giwa Barak dake garin Maiduguri suka kubutar da mutanensu, sai suka fitar da faifan video mai tsawon 1:35:24, kafin su nuna yadda suka kaddamar da harin, Shekau yayi jawabai, inda a cikin jawabin nasa na gutsuro daidai inda ya ambata da bakinsa akan cewa shine yasa aka kashe Albaniy Zaria, ga abinda yace kamar haka;

"...Democracy wannan kuka kasa ganewa cewa kafurcine dole sai kunyi? to kuje, muma muyi, malamanku dinnan duka zamu kashe, wai na kashe Albaniy har da nunawa a jarida, zan kashe (malaman) duka, eh zan kashe, ba wanda bazan kashe ba..", -inji Shekau, don haka ko yanzu aka kama Shekau shine za'a tuhuma da alhakkin kisan malam Albaniy
Cikin hotunan da na daura a wannan rubutu, hoto mai lamba na uku (3) shine wanda Shekau yasa yaje ya jagoranci kisan sheikh Albaniy Zaria, sunansa MUJAHID Abu Hanifa, yana daya daga cikin manyan yaran su Mustapha Chad da Kaka Allai (mun bada bayanin Mustapha Chad cikin rubutun da muka gabatar kwanaki kadan da suka gabata), daga baya shi wannan Mujahid Abu Hanifa ya zama cikin manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram bayan mutuwar su Mustapha Chad, ya taba samun rauni har aka yanke masa kafa daya, kafin shima Shekau yasa aka kashe shi a farkon shekarar 2016
Har ila yau shi wannan 'dan ta'adda Mujahid Abu Hanifa da kuke ganin hotonsa da bakinsa ne ya bayana cewa shine ya jagoranci kisan sheikh Albaniy Zaria kuma karku manta a lokacin yana matsayin babban kwamanda ne, daga karshe Shekau yasa aka kashe shi rana daya da Abu Maryam Al-I'ilamy shugaban cibiyar al-ghuraba'u wanda yake shine shugaban masu harhada faifan video na kungiyar Boko Haram gaba daya, hotonsa ne na daura anan mai lamba na farko (1)

Dangane da kisan malamai don Allah ku saurari karatun Muhammad Yusuf da yayi a lokacin da wasu mabiyansa sukace ai bai kamata su kafirta dukkan al'umma ba domin akwai "Al-uzuru biljahal', a ciki Muhammad Yusuf ya bayyana karara cewa su idan suka tada yaki to da 'yan izala zasu fara.

A cikin kaset din da M. Yusuf yayi mai taken "open letter' yace idan sukace malaman gargajiya to suna nufin malaman izala ne (ahlussunnah), kuma yace su ba malaman Allah bane malaman gomnatine malaman demokaradiyya
Kuma kowa yana da masaniyar cewa kaf cikin malaman sunnah da muke dasu a Nigeria babu wadanda suka san sirrin 'yan Boko Haram kamar sheikh Ja'afar da Albaniy Zaria, ta yaya 'yan ta'addan Boko Haram da masu tallafa musu zasuci nasara idan ba'a kawar da malaman daga doron duniya ba?, don haka ba makawa sune suka kashe su wallahi.

To yau an wayi gari rundinar 'yan sandan Nigeria wai ta gano wata takarda da ta samu a gidan sanata 'Danjuma goje wanda wai takardan tana kunshe da wasu bayanai dake bayyana yadda tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau ya tsara kisan Sheikh Ja'afar, wannan al'amarine na bincike da shari'ah, ni dai a kashin kaina har yanzu zuciyata bata yarda da wannan zargi da akeyiwa wannan bawan Allah Ibrahim Shekarau ba ko kadab, amma duk da haka bincike ne da kuma shari'a zai tabbatar yana da hannu a ciki ko bai dashi don babu abinda bincike ya bari sai dai idan ba'ayi ba, kuma idan har ya tabbata yana da hannu a ciki to ba makawa shima 'dan boko haram ne babba a cikin kungiyar.

Daga karshe muna jan hankalin mutane da suguji yanke hukunci akan al'amari irin wannan batare da an gabatar da bincike anje gaban alkali an tafka muhawara alkali ya yanke hukunci ba.

Munaso jama'a su fahimci cewa akwai banbanci tsakanin zargi da aikata laifi, dole ayi zargi idan aka aikata ta'addanci akan manyan bayin Allah irinsu Malam Ja'afar da Albaniy Zaria, ba laifi bane watakila don an zargi shugaban da yake da alhakkin tsaron rayukan 'yan kasa a lokacin da aka aikata ta'addanci akan wasu 'yan kasa masu matukar muhimmanci ga al'umma Sannan akan wannan al'amari dole rundinar 'yan sanda ta gabatar da kara a gaban kotu, kuma lallai dole shima Ibrahim Shekarau ya hanzarta zuwa kotu idan har yasan bashi da hannu a ciki kotu ta wankeshi
Allah Shine cikekken masani akan komai, kuma Shi (Allah) muke roko ya bayyana gaskiya a cikin wannan al'amari

No comments:

Post a Comment